Gaskiyar Lamari Kan Korar Daliba Rahama Sa'idu Daga Makarantar Koyan Aikin Jinya Ta Jihar Kebbi: 👇 Daga Ahmad Nagudu Wannan yarinyar da hotunanta ke kasa mai suna Rahama Sa'idu da labarin ta ya yadu a shafukan Sada Zumunta, bayan da ta fito a shafin ta na Instagram ta wallafa cewa wai an kore ta daga Makarantar Kimiyyar Koyon Aikin Jinya ta Jihar Kebbi, saboda kawai ta na amfani da shafukan Sada Zumunta na Yanar Gizo, wadda kuma labarin ya fantsama duniya a haka, karya ta ke game da abun da ta shaidawa duniya kan dalilin korar ta daga Makarantar nan. Asalin sunan ta shine Ramatu, ba kamar yadda ta canja ta mayar da shi Rahama ba. Iyayen ta Yarbawa ne da su ka fito daga Ibadan ta Jihar Oyo, amma a kauyen Ribah aka haife ta da ke Karamar Hukumar Zuru ta Jihar Kebbi. A nan ta tashi ta girma, kowa na ta a can ya ke. Mahaifin ta sana'ar tukin mota ya ke yi, duk da ya taba wasu ayyukan kamin wannan. Duk da ina ganin sunan yarinyar nan Rahama kuma Sa'idu, wallahi ban taɓa zat