Ƴan Sanda Sun Harbe Wani Ɓarawon Akwatin Zaɓe A Jihar Kogi
Yan Sanda Sun Harbe Wani Ɓarawon Akwatin Zaɓe A Jihar Kogi
Wasu ƴan daba sun yi yunƙurin ƙwace akwatin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.
Wakilin Alfijir Hausa ya bayyana cewar: "An kashe wani ɗan daba mai kimanin shekaru 36 yayin da wasu su ka samu raunuka lokacin da su ka yi arangama da wasu Ƴan Sandan Najeriya a ƙoƙarin su na sace Akwatin Zaɓe.
Sai dai har yanzu ba a iya tantance ko ƴan wace jam'iyyar ne ƴan daban su ka kawowa rumfar zaɓen hari da sunan yin awon gaba da Akwatin Zaɓen ba.
Matashin da ƴan Sandan su ka hallaka kan yunƙurin satar Akwatin, an bayyana sunan sa da Ojochemi Akayaba, wadda kuma bai daɗe da kammala yi wa ƙasa hidima na NYSC ba.
Comments
Post a Comment